Rashida Dangin Miji Lyrics

Allah nufeni da Haihuwa

Akan ban haihu ba dangin miji suka takuran
La ila hina nufeni da haihuwa

Akan ban haihu ba dangin miji suka takuran
Yaila hina nufeni da haihuwa

Ya Allah Rahimi
Yau na shiga zullimi
Ni ake wa tsangwami
A nai mini tsegumi
Dan ban haihu ba
Zama na gidan miji a yau shine zai gagaran
Ya ila hina nufeni da haihuwa

Siruka bata so ni ba
k__a ba laifin ta ba
Ban haifa mata jika ba
Shi yasa bata so ni ba
Dan ban haihu ba
Allan da Ya yo ni, na san k__a shine za ya ban
Ya ila hina nufeni da haihuwa

Miji na baya nan
Da miji na ya na nan
Komai zai mini nan da nan
Kaya, shi zai a da nan, Ko ban haihu ba
Ni na san da miji na na nan zai tausa yan
Ya ila hina nufeni da haihuwa

Allah nufeni da Haihuwa

Wahala ta san jiri
Zani mace a cikin gari
Ga jama'a na cikin gari
kowa ne mini ?*zazzari*?
Don basu kini ba
ko mai ke faruwa na san Allah shine ya kaddaran
La ilahina nufeni da Haihuwa

Ni dai yau na gaji
Allah yai mini agaji
Kai ne kayi gani da ji
Zan saka roko na gaji
Kai ne Ya Rabba
Roko na haihuwa na ke so ya Allah Ka ban
Ya ila hina nufeni da haihuwa

(c)2006
Ibrahim Jamilu
Freedom Radio

See also:

78
78.116
Rembrants I'll be there Lyrics
Bjork hypperballad Lyrics